1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangama a ƙasar Guinea Conakry

January 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuTw

Mutane 4 su ka rasa rayuka jiya a ƙasar Guinee, a yayin arangamar da ta haɗa jami´an tsaro da masu zanga-zanga, a birnin Nzerekore, da ke kudancin ƙasar.

Daga farkon wannan zanga-zanga, ranar 10 ga watan da mu ke ciki, zuwa yanzu, baki ɗaya mutane 9 su ka riga mu gidan gaskiya.

A ƙalla mutane dubu 5 su ka shirya wani taron gangami, bisa gayyatar ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar, dake gwaggwarmayar gwamnati ta biya masu buƙatocin su, da su ka jiɓanci naɗa saban Praministan riƙwan ƙwarya, da kuma kyautata rayuwar ma´aikata da na al´ummar ƙasa.

Saidai shugaban ƙasa Lansan Konnte, da ke bisa karagar mulki, tun shekaru 23 da su ka wuce, ya hau kujera naƙi wajen shafe hawayen ma´aikatan.

Don taimakawa a ciwon kan wannan rikici, shugaban ƙasar Senegal Abdulahi Wade, da takwaran sa na Nigeria Olesegun Obasanjo, sun yi tayin shiga tsakani.