1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangama tsakanin magoya bayan Hamas da na Fatah

May 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buxe
A ci-gaba da gwagwarmayar iko da dakarun tsaron Falasdinawa, an sake yin musayar wuta tsakanin sabuwar rundunar gwamnatin Hamas da dakarun kungiyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas. ´Yan sanda sun ce mutane da dama sun samu raunuka sakamakon musayar wutar da aka yi a birnin Gaza. Abbas wanda rundunar ´yan sanda ke goyawa baya, ya sake yin kira ga gwamnatin Hamas da ta rushe sabuwar rundunar tsaron da ta kafa. To amma FM Falasdinawa Isma´ila Haniyeh ya yi watsi da wannan kira. A kuma halin da ake ciki jami´an tsaron kan iyakar Falasdinu sun kwace tsabar kudi sama da Euro dubu 600 daga Abu Zuhri babban jami´i a kungiyar Hamas. An kame Zuhri ne lokacin da yayi kokarin tsallake kan iyakar Masar da Zirin Gaza. Doka ta bukaci Falasdinawa dake son tsallake kan iyakar da makudan kudade da su bawa jami´ai notis na sa´o´i 24, to amma Zuhri bai yi haka ba.