1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ASIA A YAU: BAYAN TSUNAMI.

January 5, 2005

WATA MACE A MATSUGUNAN YAN GUDUN HIJIRA A KASAR THAILAND TANA KOREWA DANTA SAURO.

https://p.dw.com/p/Bvdo
Hoto: AP

To a yanzu haka dai bayanan da suka iso mana sun nunar da cewa babban abin da yafi daukar hankali a yau game da girgizar kasa da kuma ambaliyar ruwa ta tsunami data shafi kasashen kudancin Asia da gabashin Africa shine na mayar da hankali da kasashen turai sukayi a yau na gudanar da shiru na mintoci uku don nuna alhini da kuma girmamawa ga wadanda suka rasa rayukan nasu sakamakon faruwar wan nan abu.

Daukar wan nan mataki dai ya biyo bayan kiran da kasar Luxembourg tayi ne ga kasashe mambobi na kungiyyar ta Eu 25 dasu gudanar da wan nan shiru na dan mintoci.

Kasar dai ta Luxembourg tayi wan nan kiran ne a matsayin ta na kasar dake rike da jagorancin tafiyar da kungiyyar ta Eu na karba karba na tsawon watanni shida masu zuwa.

Rahotanni da suka iso mana sun shaidar da cewa ana gudanar da wan nan shirun ne na dan mintoci a hukumomin gwamnati da makarantu da shagunan saye da sayarwa da kuma cikin gidajen kwanan mutane dake nahiyar ta turai.

A waje daya kuma fadar vatican dake birnin Rom na kasar italiya ma ba a barta a baya ba wajen shiga jerin gwanon gudanar da addu,oi ga ilahirin mutanen da suka rasa rayukan nasu sakamakon wan nan balai na igiyar ruwan ta tsunami

Ya zuwa yanzu dai bayanai sun tabbatar da cewa yawan mutanen da suka rasa rayukan nasu ya kara karuwa akan na baya da a yanzu jumlatan ya tashi izuwa sama da dubu dari da sittin.To amma wata majiya mai karfin gaske tayi nuni da cewa yawan mutanen da suka rasa rayukan nau ka iya kaiwa dubu dari biyu nan da yan kwanaki kalilan masu zuwa.

A yanzu haka dai ma,aikatan bayar da agajn gaggawa na can naci gaba da gudanar da aikin su a kasashe goma sha biyu da wan nan abu ya rutsa dasu a yankin na asia da kuma gabashin nahiyar Africa.

Babban abun da wadan nan maaikata sukafi mayar da hankali kai shine na samar da Abinci da ruwan sha da kuma muhalli ga wadan da suka tsira da rayukan su a wadan nan kasashe goma sha biyu.

A waje daya kuma rahotanni da suka iso mana daga kasar Indonesia inda wan nan balai yafi yin ta,adi mai munin gaske sun tabbatar da isowar sakataren mdd Kofi Anan izuwa kasar Don halartar taron kolin kokon bara na kasa da kasa da za a gudanar a gobe alhamis idan Allah ya kaimu.

Bugu da kari rahotanni daga kasar sun nunar da cewa shirye shirye sun kusan kammala game da gudanar da wan nan katafaren taron kolin duniya a gobe alhamis din.

Tuni dai da yawa daga cikin shugabannin kasashen duniya suka nuna amannarsu ta halartar wan nan taro na gobe Alhamis din.

Game da kuwa da yadda kasashen duniyar keci gaba da bayyana karin yawan kudin tallafi da suke bawa wadan nan kasashe a yanzu haka kasar Jamus ce tafi ta zakka a tsakanin kasashen duniya wajen bada wan nan tallafi da a yanzu kudin da suka bayar ya kai a kalla yuro miliyan 500.

Daga kasar Jamus din kuma sai kasar Japan mai dalar Amurka miliyan 500 kana daga nan sai kasar Amurka mai Dala Miliyan 350.

Ya zuwa yanzu dai tsoffin shugabannin kasashen Amurka da kuma shugaba maici da sauran shugabannin kasashen duniya naci gaba da kiraye kirayen mutane da kamfanoni masu hannu da shuni dasu tallafawa wadan nan kasashe da abin da Allah ya sawake musu don inganta rayuwar wadan da wan nan balai ya shafa.

Ibrahim Sani.