1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atisayen sojin Afrika a Mali

August 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuDT

A yau a ƙasar Mali ake gudanar da wani Atisayen soji wanda ya haɗa da sojojin Amurka dana ƙasashe goma sha uku na Afrika da kuma wasu ƙasashen turai. Kimanin sojoji 350 ne ke halartar atisayen na bana wanda Amurka ta tsara da nufin bada horo ga sojojin Afrika domin samun ƙwarewa ta sanin makamar aiki. Zaá ci gaba da atisayen har ya zuwa ranar 8 ga watan Satumba. Zai kuma gudana ne a birnin Bamako na ƙasar Malin. Ƙasashen dake halartar atisayen sun haɗa da Algeria da Chadi da Mauritania da Morocco da Niger da Nigeria da Senegal. Sauran sune Tunisia da Mali da Burkina faso da Faransa da Netherlands da kuma Britaniya.