1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Au na kokarin samon bakin zaren game da Fadada Mdd

October 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvNe

Kungiyyar hadin kann nahiyar Africa wato Au, tace zata gudanar da wani taron koli a ranar litinin mai zuwa don cimma matsaya guda a game da shirin nan da ake na fadada mdd.

A dai lokacin wannan taro , ana sa ran kwamitin kasashe goma da aka kafa karkashin shugaban kasar Saliyo, wato Tejan Kabbah zai mika rahoton sa a game da nauyin da aka dora masa na samo bakin zaren barakar da aka samu a tsakanin kasashen na Africa.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa matukar kasashen na Africa basu cimma matsaya guda ba a game da wannan batu to babu shakka da wuya a samu kaiwa da kokarin fadada kwamitin sulhun na Mdd.

An dai samu sabani a tsakanin kasashen na Africa ne da kuma takwarorin su wasu G4 a game da tsarin fadada Mdd.

Su dai kasashen na Au na son a fadada kwamitin sulhun Mdd ne da kujeru 10, shidda daga cikin su zaunannu tare da karfin hawa kujerar naki.

Su kuwa kasashen na G4 na da ra´ayi irin na kasashen na Africa , amma kuma banda bawa sabbin kasashen karfi na hawa kujerar nakin.

Shugaban kungiyyar ta Au,wanda kuma shine shugaban Nigeria, wato Olesegun Obasanjo ya bukaci kasashen na Africa dasu gaggauta cimma matsaya guda ko kuma duka kowa ya rasa.