1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU na son a tsaurara tsaro a Burundi

Ahmed SalisuMay 21, 2016

Kungiyar kasashen Afirka ta AU ta bukaci da a tura karin jami'ai da za su sanya idanu kan halin da ake ciki a Burundi wadda rikicin siyasa ya dabaibaye.

https://p.dw.com/p/1IsDL
Burundi Pierre Nkurunziza
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Karaba

Masu bincike na kungiyar tarayyar Afirka AU kan hakkin dan Adam suka ce akwai bukatar da ke akwai ta ganin an tura jami'an 'yan sanda na kasa da kasa zuwa kasar ta Burundi baya ga wasu jami'an da AU din ta rigaya ta tura.

AU din ta ce 'yan sanda za su taimaka wajen karfafa tsaro a kasar da kiyaye rayukan mutane musamman ma a wuraren da suka yi kaurin suna yanzu haka wajen fuskantar tashin hankali.

Wannan butaka ta kungiyar ta AU dai na zuwa ne gabannin hawa teburin sulhu da za a yi kan rikicin kasar ta Burundi a birnin Arusha na Tanzaniya sai dai rahotanni na cewar za a yi zaman ne ba tare da wakilan 'yan adawa ba.