1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AU na kokarin shawo kan rikicin Burundi

Lateefa Mustapha Ja'afarDecember 18, 2015

Kwamitin tsaro da wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka AU, ya yanke shawarar tura dakarun wanzar da zaman lafiya 5,000 zuwa kasar Burundi.

https://p.dw.com/p/1HPVl
AU-Gipfel in Addis Abeba Äthiopien
Hoto: Imago

Wani wakili a kungiyar ta AU da ya halarci taron da ya tattauan kan batun tura sojojin ya shaidawa manema labarai cewa, kwamitin ya yi amfani da dokar da ta bai wa kungiyar ta AU damar tura dakarun wanzar da zaman lafiyar ba tare da sanar da shugaban kasar ta Burundi ba. An dai gaza samun damar jin ta bakin fadar shugaban kasar ta Burundi da a baya ta yi watsi da batun tura dakarun wanzar da zamn lafiyar. Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundin dai na da wa'adin sa'o'i 96 ya bayyana ra'ayinsa dangane da batun tura sojojin na AU, wanda ake sa ran za su rattaba hannu kansa nan da 'yan kwanaki.