1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU zata tura dakarun tsaro a Comoros

Zainab A MohammadMarch 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7J

Kungiyar gamayyar afrika AU ta amince da tura dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa tsibirin Comoros dake fama da ringimu na barazanar juyin mulki ,tare da tabbatar dacewa babu hannu dakarun kasar cikin zaben shugaban kasa da zai gudana ranar 14 ga watan mayu.Wadannan tawaga na kungiyar dai da zaa kirasu AMISEC a takaice,zasu hadar da masu lura da zabe da masu gani da ido,wadanda zasu kunshi sojoji da fararen hula 432,da wasu jamian yansan 30.Ana saran cewa tawagar jamian zasu kasance a Comoros kafin zaben fitar da yan takara dazai gudana ranar 16 ga watan gobe,zaben dazai gudana a tsibirin Anjuan.A karkashin kundun tsarin mulki na hadin kann kasa,ana bukatar alummar tsibirin su zabi 3 daga cikin yantakara 14 ,da zasu nemi kujeran shugabancin hadin kann tsibran.Kungiyar ta AU dai na fatan cewa ,alumman tsibiran zasu gudanar da wannan zabe ba tare da wata matsala ba.