1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aung San Suu Kyi da batun zaɓe a ƙasarta

August 24, 2010

Madigar adawa ta Bama ta bukaci 'yayan wannan ƙasa da su iya tsayuwar daka domin hana maguɗi a zaɓen 7 ga watan nowamba.

https://p.dw.com/p/OvAW
Aung San Suu KyiHoto: AP

Sananniyar 'yar adawar nan ta ƙasar Bama wato Aung San Suu kyi, ta yi kira ga 'yan ƙasarta da su raka,su kuma tsare ƙuri'un da za su kaƙa a lokacin zaɓen da zai gudana a watan nowamba mai zuwa. Lawyan da ke magana da yawun Suu kyi da ta taɓa lashe lambar zaman lafiya ta NOBEL, ya ce ta bukaci 'yan Bama da su ƙalubalanci duk wani sakamako na boge da za a wallafa.

Ita dai madigar 'yan adawan bama- ba ta samu damar tsayawa takara ba, saboda rashin cika sharudan da hukumomi suka gindaya, da kuma rusa jam'iyarta ta LDN da suka yi. Shekaru 20 'yar adawar ta shafe tana tsare a gidanta, a wani mataki na hana ta duk wata walwala a harkokin siyasa.

Ana ci gaba da samun rarrabuwan kawuna tsakanin magoya bayanta game da wasu manufofinta na siyasa. Amma ta ce wannan ba zai hana sa ido a zaɓen na bakwai ga watan Nowamba ba, matikar dai ana son ɗora kasar ta Bama kan turbar demokaradiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Ahmed Tijjani Lawal