1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aung San Suu Kyi ta kira Rohingya 'yan ta'adda

Salissou Boukari
September 6, 2017

Jagorar gwamnatin kasar Myanmar Aung San Suu Kyi ta soki abin da ta kira yada labarai na karya da ake yi kan halin da tsirarun Musulmi 'yan Rahingya ke ciki a kasar.

https://p.dw.com/p/2jSvm
Myanmar Aung San Suu Kyi in Wundwin
Jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu KyiHoto: Reuters/S. Lewis

Kasashen duniya sun yi ca a kanta ta dalilin shirun da ta yi ba tare da ta ce uffan ba kan kisan kiyashin da sojojin kasar ta Bama ke yi wa tsirarun kasar na Rohingyas. Yayin wata hira ce da ta yi ta wayar tarho tare da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Aung San Suu Kyi ta ce ruruta lamarin ne da ake yi ya sa kasashen duniya ke nuna tausayi ga Musulmin na Rohingya da su suke daukan su a matsayin 'yan ta'adda.

A cewar kungiyoyin agaji ya zuwa yanzu an samu akalla mutane 146,000 'yan Rohingya da suka yi gudun hijira zuwa Bangaladash tun daga ran 25 ga watan Augusta da ya gabata kawo yanzu, yayin da wasu dubbai ke kan hanya, wasu kuma an taresu a kan iyakar kasar ta Bangaladash.