1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayar tambaya a dangane da yancin yan jarida a Jamus

August 3, 2007

Binciken yan jarida 17....

https://p.dw.com/p/BvSm
Jaridu
JariduHoto: picture-alliance/dpa

Ana cigaba da gudanar da mahawara anan tarayyar jamus dangane da wasu yan jarida guda 17 da ake zargi da laifin yayata wasu bayanan sirri na hukumar asirin kasar.

Yanzu haka dai wannan mahawara tana cigaba da gudana,musamman a bangaren komitin da aka nada a ta musamman daga majalisar dokokin kasar domin tafiyar da binciken.Haskan kuma ya haifar da da wani sabon babi adangane da yancin yan jarida wajen tafiyar da ayyukansu,da harkokin tsaro a hannu guda kuma da cigaban da kamfegn da akeyi na yaki da ayyukan tarzoma.

Yan siyasa daga jammiyyun adawa da kuma kafofin yada lamabarai na wayannan yan jarida suka fito nacigaba da yin korafi dangane da wannan batu.

Bisa ga kundun tsarin mulkin jamus dai,yan jarida nada yanci tafiyar da aikinsu,kuma baa yarda a shiga tare da binciken kayayyakin aikin yan masanaantar yada labaru ba.Amma duk da haka a yan shekaru da suka gabata yan jaridar dake wannan kasa sun fuskanci uire iren wannan bincike.Acewar mai magana da yawun kungiyar yan jarida ta kasa Henridrik Zörner,batun na neman wuce gona da ari…

“Bisa dukkan alamu baa sake laakari da yan jarida kamar yadda ya kamata,batun yan cin yan jarida kuwa babu alamunsa,a wannan yanayi da ake tafiya,an mayar dasu wani matsayi na daban.Yanzu ana cikin wani hali mai sarkakkiya,tunda a yanzu wakilin majalisar dokoki,akarkashin amincewar mafi yawa daga cikinsu,suka cimma matsaya makamancin wannan”

Komitin binci ta tarayyar jamus din dai,da amincewar mafi yawa daga cikin membobinta sun zartar dacewa,kowane bayani dake kunshe da batutuwan sirri adangane da batun kamfen na yaki da ayyukan tarzoma,ko makamancinsa zai iya kasancewa a baiyanar jamaa.Volker Kauder na jammiiyyar CDU,shine shugaban komitin binciken…

“Yace mutum na iya sanin bayanai dangane da wasu batutuwa na musamman ta hanayar karatun jaridu,kamar yadda muda muke wannan komiti muka sani..”

Mafi yawa daga cikin yan jamiiyyar adawa dai na ganin cewa yan jaridan nada hanyoyi daban bisa ga tsarin aikinsu na sanin bayanai kan batutuwa da dama,kuma kasancewar suna da yanci na tafiyar da ayyukansu,zasu iya yayata bayanai da suka ga ya dace jamaa su sani ko su karanta.

Tun dai a watan febrairu ne kotun kundun tsarin mulkin kasa a nan jamus,ayayin shariar jaridar dake ruwaito harkokin siyasa Cicero ,ta sake bayanai dangane da batun yancin da yanjarida suke dashi ayayin tafiyar da ayyukansu.