1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan cibiyar ba da lamuni ta Jamus akan matakan taimakon rayawa

November 8, 2004

Cibiyar ba da lamuni domin ayyukan raya kasashe masu tasowa ta samu nasarori a matakan tallafi da take dauka a cikin shekaru biyun da suka wuce, a cewar wani rahoton da sashen bitar ayyukan cibiyar ya bayar

https://p.dw.com/p/Bveq

An samu nasarori masu yawan gaske akan kashi 94% na shirye-shirye kimanin 127 da aka tallafa musu da kudi na Euro miliyan dubu da dari daya a tsakanin shekara ta 2002 da shekara ta 2003. Duka-duka shirye-shirye guda goma ne kacal kwalliya ba ta mayar da kudin sabulu game da su ba. A lokacin da take bayani a game da rahoton sashen binciken ayyukan bankin ba da lamuni domin ayyukan gudanarwa na Jamus, ministar taimakon raya kasashe masu tasowa Heidemarie Wieczorek-Zeul tayi nuni da ire-iren ci gaban da ta nakalta a ziyarar da ta kai baya-bayan nan ga kasar Ruwanda inda sharadin da aka shimfida na daukar nagartattun matakan yaki da talauci da bin manufofi na demokradiyya domin yafe basusukan da ake bin kasashe ‚yan rabbana ka wadata mu ya taimaka matuka ainun, inda a kasar ta Ruwanda yanzu haka yara ke da ikon samun ilimi na faramare. A kasashe kamarsu Muzambik da Tanzaniya ma an samu ribanyar yawan yaran dake halartar ajujuwan makarantun faramare sakamakon yafe musu basusukan da aka yi bisa sharadin daukar nagartattun matakai na yaki da talauci. A dai wannan marra da muke ciki yanzu haka Jamus ce akan gaba a matakan bitar ci gaban da ake samu a shirye-shiryen raya kasashe masu tasowa, kamar yadda kwararrun masana na bankin duniya suka nunar. Wani muhimmin ci gaban da ake samu a wannan bangaren shi ne matakan tallafi ga kanana da kuma matsakaitan ‚yan kasuwa masu zaman kansu. Kazalika da manoma, wadanda ke da ikon sayen dabbobi daga ‚yan kananan kudaden rance da ake kaddamar musu. An ji wannan bayanin ne daga bakin Hans-Rimbert Hemmer, shugaban sashen bitar ayyukan bankin rayawar na Jamus, wanda ya kara da cewar:

A cikin shekarun baya-bayan nan mun bi diddigin wasu shirye-shirye da suka shafi tallafi na kudi ga kananan manoma, inda muka gano cewar a hakika an samu kyakkyawan ci gaba wajen tallafa wa masu karamin karfi, wadanda ba su da ikon neman rancen kudi daga bankuna da sauran cibiyoyin rance, ballantana su samu isasshen jarin da zai ba su ikon bunkasa ayyukansu da kuma fita daga kangin talauci.

To sai dai kuma duk wannan ci gaba akwai kuma wasu sjirye-shiryen wadanda murna ta koma ciki a game da su. Misali hare-haren da akan kai akan matatun ruwa a yankunan da ake fama da yake-yaken basasa a cikinsu. Amma irin wannan koma baya ba abu ne da zai hana ruwa gudu ko ya sanyaya guiwa a bisa manufa ba, in ji ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemari Wieczorek-Zeul.