1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan kungiyoyin agaji masu zaman kansu a Iraki

April 15, 2004

Kungiyoyin taimakon jinkai masu zaman kansu na cikin hali na kaka-nika-yi a kasar Iraki sakamakon rashin tabbas a game da tsaron lafiyar ma'aikatansu

https://p.dw.com/p/Bvkf
Tabarbarewar tsaro a Iraki
Tabarbarewar tsaro a IrakiHoto: AP

A ‚yan kwanakin da suka wuce jaridar Al-Hayat ta fito fili tana mai kwatanta halin da ake ciki a kasar Iraki a yanzun da yakin basasar da aka fuskanta a kasar Lebanon. A wancan lokaci garkuwa da mutane da kuma amfani da su domin yada farfaganda ta kafofin yada labarai abu ne da ya zama ruwan dare a kasar ta Lebanon. A baya ga haka wakilin da MDD ta tura domin neman sulhu a kasar Iraki, Lakhdar Ibrahimi, shi ne babban jami’in da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa tayi masa aike zuwa Lebanon domin shiga tsakani da sasanta rukunonin kasar da ba sa ga maciji da juna. Ta la’akari da haka ba zama abin mamaki ba ganin yadda ake marhaban lale da ‚yan gudun hijirar Iraki dake komawa gida daga kasar Lebanon, saboda cikakkiyar masaniyar da suke da ita wajen harhada bamabamai da kai farmaki kan motocin dake cike da fasinjoji, a cewar jaridar ta Al-Hayat. A kuwa lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa, Frank McAreavey, ma’aikacin kungiyar taimakon jinkai ta Jamus mai suna Help, cewa yayi:

Kwana daya kafin tasowarmu, daya daga cikin ma’aikatanmu ya yi wa takwaransa rakiya zuwa filin jiragen sama kuma akan hanyarsa ta dawowa ya tsallake rijiya da baya daga wani hari na bom. Wannan tsautsayin tuni ya zama ruwan dare a kasar Iraki. Amma dangane da wannan sabon salo na garkuwa da mutane, shi ne ainifin abin da ya tsorata mu. Zamanmu a kasar ba ya da amfani muddin ba mu da ikon fita waje. Saboda ba za a iya raba wa mutane kayan taimakon da suke bukata ba.

A hakika kuwa babu wani abin da ya banbanta halin da ake ciki a Irakin da wanda aka kasance ciki a Lebanon ko Vietnam ko kuma Mogadishu a Somaliya. A garin Falluja kadai an kiyasce yawan mutanen da suka yi asarar rayukansu zai kai mutum 600, a baya ga wasu sama da dubu daya da suka ji rauni da kuma wasu dubu biyar da suka tagayyara. Dukkan kungiyoyin agaji da na kare hakkin dan-Adam na batu a game da wata mummunar masifar da ta rutsa da kasar Iraki. Kungiyoyin sun shiga kaka-nika-yi. Domin kuwa a daidai wannan lokaci ne ake bukatar taimako daga garesu ruwa a jallo, amma a daya bangaren ba zasu iya gudanar da ayyukansu ba ta la’akari da tabarbarewar al’amuran tsaro. A cikin bayanin da yayi Frank McAreavey ya kara da cewar ala-tilas ma’aikatan taimakon suka shiga zaman kulle a gidajensu. Da farko ba su so tashi daga kasar ta Iraki ba har sai sun ga yadda al’amura zasu kasance. Amma tun bayan da ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta yi musu gargadi karo na biyu domin su tashi daga kasar sakamakon kisan gillar da aka yi wa jami’an tsaron nan guda biyu makon da ya gabata sai suka ga ba Sarki sai Allah, tilas suka bar kasar kuma ba zasu koma ba sai bayan da kura ta lafa kuma aka samu sararawar al’amura.