1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan ´Yan ta´adda na ci gaba da zafafa a Saudiya

Ibrahim SaniNovember 28, 2007
https://p.dw.com/p/CUJv

Jami´an tsaro a Saudiya sun cafke wasu mutane 203, bisa zargin shirin kai hare haren ta´addanci. Bugu da ƙari an kuma zargi mutanen da ƙoƙarin kai hare hare kan bututun mai na ƙasar. Mutane 22 daga cikin waɗanda aka kamen a cewar rahotanni,ƙwararrune wajen harba makamai ma su linzami. Ma´aikatar cikin gida ta Saudiyan ta zargi mutanen da ƙoƙarin shigowa da muggan makaman izuwa cikin ƙasar, don amfani da su wajen kai hare haren.Koda a makon daya gabata sai da wasu tsageru 7 su ka yi ƙoƙarin kai hari kan wasu bututun mai dake gabashin ƙasar.