1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baƙin jinin 'yan Nijeriya a Afirka ta Kudu

June 18, 2010

A daidai lokacin da ake ci gaba da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ana kuma saka ayar tambaya game da abin da ya haifarwa da 'yan nijeriya baƙin jini a wannan ƙasa

https://p.dw.com/p/Nx0F
Ana ci gaba da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya a Afirka ta KuduHoto: AP

A dai halin da ake ciki yanzu wasanni sun yi zafi a gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya da ake gudanarwa a Afirka ta Kudu. To sai dai kuma har yanzu ba a ga gwarzon namiji kuma uban ƙasar Afirka ta Kudun Nelson Mandela walau a bikin buɗe gasar ko kuma tsakanin 'yan kallo a wasanni biyu da ƙasar tayi ba. A sakamakon haka jaridar Die Zeit take saka ayar tambaya a game da iya tsananin rashin lafiyar Nelson Mandela inda take cewar:

"Da dai Mandela ya halarci bikin buɗe gasar da hakan ya ƙara wa shagulgulan armashi matuƙa da aniya. Amma kuma duk da baƙin cikin da mutane ke yi game da rashin halartar tasa a ɗaya ɓangaren kuma ana tattare da fagaba a game da iya tsananin rashin lafiyar tsofon shugaban Afirka ta Kudu ma'abuci dattaku. A jajibirin buɗe gasar dai taɓa kunnensa Zenani ta mutu sakamakon hatsarin mota. Hakan ya jefa dukkan dangin Mandela cikin makoki a yayinda ƙasar ke cikin ɗoki da murna. A baya ga ainihin rashin lafiyar da yake fama da ita da ire-iren waɗannan abubuwa na baƙin ciki da kan rutsa da danginsa, kazalika Nelson Mandela na fama da wasu 'yan ciwace-ciwace sakamakon shekaru 27 da yayi a gidan kurkuku."

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a cikin nata sharhin dangane da yayata maganar miyagun laifuka da aka riƙa yi kafin gabatar da gasar ƙwallon ƙafar ta cin kofin duniya a Afirka ta Kudu cewa tayi:

"Ko shakka babu Afirka ta Kudu ƙasa ce mai haɗarin gaske dangane da miyagun laifuka, amma fa ire-iren rahotannin da kafofin yaɗa labarai suka riƙa yayatawa na ban tsoro a game da wannan ƙasa, wuce gona da iri ne kawai. Bisa ga dukkannin alamu ma dai an samu kyatatuwar al'amuran tsaro ga illahirin al'umar ƙasar sakamakon gasar ta cin kofin duniya."

Ɗaya daga cikin abubuwan dake ci wa jama'a tuwo a ƙwarya a game da gasar ƙwallon ƙafar ta cin kofin duniya dai shi ne kakakin nan na Vuvuzela da 'yan kallo ke busawa a filin wasa. Bisa ta bakin jaridar Berliner Zeitung dai ra'ayi ya kasu ne gida biyu tsakanin masu goyan baya da masu adawa da wannan kakakin, galibi Turawa, waɗanda ke famar kiran ganin an haramta Vuvuzela tsawon lokacin waɗannan wasanni wai saboda barazanarta ga dodon kunne. Amma kuma a ɗaya ɓangaren masana kimiyyar tarihi sun nuna cewar Vuvuzela na daga cikin tsaffin al'adu na ɗan-Adam kamar dai busa ƙaho da ire-irensu da aka gada tun zamanin kakannin-kaka.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta bayyana mamakinta ne a game da asbin da ya haifarwa da 'yan Nijeriya baƙin jini a Afirka ta Kudu inda ta ce:

"'Yan Nijeriya na da baƙin jini a Afirka ta Kudu. Amma kuma hakan na da dangantaka da hannu dumu-dumu da 'yan Nijeriyar ke da shi a ƙungiyoyin 'yan masha'a masu aikata miyagun laifuka a Afirka ta Kudun, kama daga fashi da makami da safarar miyagun ƙwayoyi da fataucin mata. Galibi a duk lokacin da aka cafke masu waɗannan masu laifuka sai an samu wani ɗan Nijeriya tsakaninsu. Hakan ya sanya ake sa wa 'yan ci ranin Nijeriyar a Afirka ta Kudu ido da kuma ɗariɗari da su ba tare da la'akari da sana'arsu ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal