1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba´a cimma matsaya ba tsakanin Abbas da Meshaal a taron Damascus

January 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuTj
Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da shugaban kungiyar Hamas Khaled Meshaal sun kasa cimma madafa a takaddamar da suke yi game da kafa wata gwamnatin hadin kan Falasdinawa. Hakan ya kara dakushe fatan kawo karshen rikicin siyasar cikin gaggawa. Jami´ai na bangarorin biyu sun ce abin da ya hana ruwa gudu a taron da aka yi cikin daren jiya ya, shi ne batun kalaman da za´a yi amfani da su cikin yarjejeniyar shirye shiryen sabuwar gwamnati. Yayin da Abbas ke son gwamnati ta yi aiki da kudurorin kungiyar kasashen Larabawa da kuma yarjeninoyin da aka cimma tsakanin Isra´ila da Falasdinawa. Amma ita Hamas ta dage kan amfani sda kalmar girmamawa wadda ba ta yi daidai da bukatun kasashen duniya ba.