1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba´a kashe ´yan al-Qaida a farmakin da Amirka ta kai Pakistan ba

January 21, 2006
https://p.dw.com/p/BvBN
Köhler da Kwasniewski
Köhler da KwasniewskiHoto: AP

FM Pakistan Shaukat Aziz ya ce masu bincike ba su gano wata shaida ba cewar ´ya´yan al-Qaida na daga cikin mutane da suka rasu a wani farmaki ta sama da Amirka ta kai kan wani kauye dake kusa da kan iyakarta da Afghanistan a karshen makon jiya. FM Aziz ya bayyana haka ne bayan taron da suka yi da babban sakataren MDD Kofi Annan a hedkwatar majalisar dake birnin New York. A saboda haka Aziz ya ce bai kamata a yi mamaki ba yadda aka yi ta gudanar da zanga-zangar kyamar Amirka a fadin kasar ta Pakistan tun bayan harin na makami mai linzami, wanda yayi sanadiyar rayukan mutane 18. Da farko kafofin yada labarun Amirka sun ce kwararrun masu harhada bama-bamai na kungiyar al-Qaida su na daga cikin wadanda aka halaka a wannan hari.