1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babatu akan Dejagah

October 10, 2007

Ana ci gaba da subatu a game da dan wasan kwallon kafar Jamus dan usulin Iran da ya ce ba zai shiga gasa da Isra'ila ba

https://p.dw.com/p/BtuP
Ashkan Dejagah
Ashkan DejagahHoto: AP

Peter Phillip ya ce wannan ba shi ne karo na farko da aka fuskanci wata matsala shigen wannan ba. Domin kuwa a shekara ta 1994 wani dan kwallon kafa daga kasar Iran dake wa kungiyar Bayern Munich wasa ya ki ya shiga wata karawar da kungiyar tayi da wata kungiya ta kasar Isra’ila a garin Tel Aviv. Amma ire-iren martanin da kafofin yada labarai da jami’an siyasa ke mayarwa a kan shawarar ta Dejagah a yanzun ba zai taimaka a samu sararawar al’amura a maganar zama na cude-ni-in-cude-ka tsakanin Jamusawa da takwarorinsu baki da aka dade ana yayatawa ba. Shi dai wannan yaron ya fito fili ya bayyana cewar a saboda dalilai na siyasa da kuma danginsa ba zai iya shiga gasar ta kungiyoyin kwallon kafa na ‘yan kasa da shekaru 21 da za a yi tsakanin Jamus da Isra’ila ba. Nan da nan jami’an siyasa na Christian Democrats da Social Democrats suka shiga korafi tare da saka ayar tambaya cewar wai shin a yanzun mun shiga wani sabon yayi ne inda dan wasa ke da ikon tsayar da shawara a game da wanda zai yi takara da kuma wanda ba zai yi takara da shi ba. Bai kamata a mayar da wasannin motsa jiki wasu manufofi na siyasa ba. Kuma duk wani dan wasan da yayi haka Ya-Allah Bajamushe ne tsantsa ko dan kaka-gida wajibi ne a kwabe masa rigar wasa ta ‘yan kasa. Ita kuwa majalisar tsakiya ta Yahudawa cewa tayi wai ba zata yiwu ba wani dan wasa na kasa ya dauki wani mataki na radin kansa domin kaurace wa yahudawa. A hakika da za a iya cewa dukkansu suna da gaskiya a game da wannan martani da suka mayar da a ce Ashkan Dejagah ya fito fili ne yana mai Allah Waddai da Isra’ila kuma ya ki shiga gasar ne saboda kyamar Yahudawa. Amma fa wannan ba shi ne dalilin shawarar da ya yanke ba. Ya ba da dalilai tare da bayyana cewar shi fa har yau yana amfani ne da takardun fasfo guda biyu na Jamus da Iran. Ta la’akari da haka dukkan wadannan masu babatun ba su da wata masaniya a game da mawuyacin hali na tsaka mai wuya da ‘yan kaka-gida dake karbar takardun fasfo na Jamus kan samu kansu a ciki. Kazalika wannan mutum bai san ma abin da ake kira zama na cude-ni-in-cude-ka ba. Zama dan kasa ba ya nufin watsi da tushe kwata-kwata, saboda mutum na da dangi da abokan arziki, watakila ma da kadarori da ya baro su a gida. Abin tambaya ma a takaice shi ne me ya sa kowane bajamushe ke da ‘yancin kulla zumunta da wata kasa ta ketare, amma dan kaka-gida baya da ‘yancin yin haka.