1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban bankin Amirka ya rage kuɗin ruwa

January 29, 2008
https://p.dw.com/p/CwP8

Kasuwannin hannayen jari a nahiyar Asiya sun ɗan farfaɗo sakamakon rage kuɗin ruwa da babban bankin Amirka ya yi. Kasuwar Nikkei a Japan ta yi sama da maki kimanin kashi 3 cikin 100 a hada-hadar kasuwanci ta yau da safe sannan kasuwar Hang Seng ta Hongkong kuma ta samu ƙarin maki na sama da kashi biyar cikin 100. Hakan ya zo bayan da babban bankin Amirka ya rage kuɗin ruwa da misalin kashi 0.25 cikin 100 ya zuwa kashi 3.5 cikin 100 a wani mataki na shawo kan matsalolin da ake fuskanta a kasuwannin sayar da hannayen jari samakon fargabar da ake nunawa dangane da koma-bayan tattalin arzikin Amirka. Wannan mataki ya taimaka an samu daidaituwar al´amura a kasuwannin Amirka da ma a Turai.