1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban hafsan hafsoshin sojin Britaniya ya yi kira ga janye dakarun ƙasar daga Iraqi.

October 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bug5

Babban hafsan hafsoshin rundunar sojin Birtaniya, Janar Sir Richard Dannat, ya yi kira ga janye dakarun ƙasarsa daga Iraqi, saboda a nasa ganin, kasancewar dakarun a can na ƙara taɓarɓare al’amuran tsaro a ƙasar. A cikin wata fira da ya yi da jaridar nan ta Daily Mail ta Birtaniyan, Janar Dannat, ya bayyana cewa katsalandan dab Birtaniyan ke yi a Iraqi na ƙara haɓaka barazanar da ake yi wa kafofin yam a sauran yannkuna na duniya. Birtaniyan dai, ita ce ’yar hannun daman Amirka da kuma muhimmiyar abokiyar burminta a Iraqin, inda a halin yanzu take da dakaru dubu 7 girke a can. Tun da aka afka wa Iraqin da yaƙi ƙarƙashin jagorancin Amirka don hamɓarad da gwamnatin Saddam Hussein a cikin shekara ta 2003 dai, sojojin Birtaniya ɗari da 19 ne suka rasa rayukansu.

A halin da ake ciki kuma, ofishin Firamiyan Birtaniya Tony Blair, ya ce ba shi da wata masaniya game da bayanan sukar laimrin ƙasar a Iraqi, da Janar Dannat ya yi. Sabili da haka babu abin da zai ce a kan wannan batun.