1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban Jami´in diplomasiyan EU Solana zai kai ziyara a Teheran

June 3, 2006
https://p.dw.com/p/BuvW

Wani labarin da ya iso mana yanzu na cewa babban jami´in na kungiyar EU ka iya kai ziyara birnin Teheran a wani mataki na shawo kan hukumomin kasar su amince da jerin taimakon da aka alkawarta musu. A gobe lahadi mista Solana zai fara rangadin yaankin GTT, inda zai gana da jami´an Isra´ila da na Falasdinawa, amma kakakinsa ya fadawa kamfanonin dillancin labaru a birnin Brussels cewa ana iya canza ajandar tafiyar don bawa Solana din damar yada zango a Teheran.