1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban kawancen nuna zumunta a Jamus

Kay-Alexander Scholz/ Mohammad Nasiru AwalFebruary 11, 2016

Kawancen kungiyoyin ma'aikata da na addinai da na al'ummomi zai yi yaki da rashin juriya da kyamar dan Adama.

https://p.dw.com/p/1Hu6I
Deutschland Allianz für Weltoffenheit Solidarität Demokratie und Rechtsstaat
Hoto: imago/epd/J. Blume

Hadaddiyar kungiyar kwadagon Jamus ce ta kirkiro da kawancen kimanin makonni biyar da suka wuce. Fatan shugaban kungiyar Reiner Hoffmann da sauran kungiyoyin tara da suka da na addinai da ke cikin kawance shi ne kiran da suka yi zai janyo hankali karin kungiyoyi da sauran masu fafatuka a Jamus da za su yi koyi da su.

Muhimman batun da suka sa gaba shi ne takaddama ko mahawarar da ake yi a kan 'yan gudun hijirar ta samar da masalaha a rika fitowa bainar jama'a ana ta babatu ko amfani da batun don cimma wata manufa a siyasance.

Yaki da masu akidar kyama

Shin mai ya sa suka zabi wannan lokaci na yin wannan kira? Zekeriya Altug shi ne kakakin majalisar gudanarwa ta Musulmi a Jamus ya nuna matukar damuwa yadda ake furuta kalaman batanci ga Musulmi da 'yan gudun hijira a Jamus.

"Mun shaida yadda ake raba kan jama'a. Muna kuma ganin yadda mahawarar game da 'yan gudun hijira ta dauki sabon salo na karkata ga masu ra'ayin rikaun kyamar baki. Maganganu da kiraye-kirayen da ake yi dangane da 'yan gudun hijirar ya samar da wani yanayi inda 'yan siyasa suka zama tamkar masu magana da yawun mafi yawan 'yan kasar."

Altug ya ce wajibi ne a dauki mataki kuma saboda haka ne aka kulla kawancen.

Reiner Hoffmann Kommentarbild App
Zekeriya AltugHoto: privat

Shi ma mataimakin shugaban majalisar tsakiya ta Yahudawa a Jamus Mark Dainow ya nuna irin wannan damuwa inda ya nuna takaicinsa ga karuwar masu kyamar baki a kasar, saboda haka ya zama wajibi a hada karfi da karfe wajen girmama juna da nuna juriya da 'yancin yin addini da kuma kare 'yancin tsiraru.

"Dole ne mu tallafa wa mutane da ke tserewa daga tashe-tashen hankula kuma suke neman mafaka a wurinmu. To sai dai abin fargaba dangane da 'yan gudun hijirar da ke zwua Jamus shi ne, suna tahowa ne da akidar kyamar Yahudanci, domin sun fito ne daga wata al'ada daban inda kyamar Yahudawa ya zama ruwan dare."

Mark Dainow ya kara cewa a saboda haka wajibi ne a yi duk iya kokarin ganin 'yan gudun hijirar sun saje da wannan al'umma.

Sako mai karfi ga masu sanya fargaba zukatan jama'a

Shi kuwa a nasa bangaren shugaban majalisar majami'u Evanjelika a Jamus, Heinrich Bedford-Strohm cewa ya yi burin da suka sa a gaba shi ne aikewa da wani sako mai karfi ga masu son amfani da batun na 'yan gudun hijira don cimma wani buri na daban.

Dr. Zekeriya Altug DITIB Nord
Rainer Hoffmann da ya kirkiro kawancen

"Ana cikin wani hali na rashin tabbas a Jamus kan yadda za a tinkari matsalar 'yan gudun hijira. Kungiyoyin kyamar baki da masu ra'ayin rikau na son su yi amfani da wannan rashin tabbas don cimma burinsu na siyasa. Saboda haka wannan kawancen zai mayar hankali kan samar da wata al'umma mai haba-haba da baki."

Ra'ayi dai ya zo daya cewa a ba da fifiko kan abubuwan da suka hada kan jama'a maimakon daga murya kan bambamce-bambamcen da ke tsakani.