1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Amr Moussa ya fara ziyara a Bagadaza

October 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvOb

Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Amr Moussa ya isa kasar Iraqi inda zai gudanar da ziyarar aikinsa ta farko tun bayan kifar da gwamnatin Saddam Hussein. Yayin wannan ziyara ta yini 3 Amr Moussa zai tattauna da wakilan gwamnati akan shirye-shiryen taron sassanta al´umar Iraqi da zai gudana a birnin Alkahira. A wani labarin kuma ´yan sandan Iraqi sun ce sun kame wani dan dan´uwar Saddam Hussein wato Yasir Sabhawi Ibrahim, wanda ake zargi da kasancewa daya daga cikin mutane dake tallafawa ´yan tawaye da kudi. A kuma can arewacin Iraqi an kai hari akan wani muhimmin bututun mai da ya hada wata matatar mai daga birnin Kirkuk zuwa arewacin Bagadaza. A ci-gaba da tashe-tashen hankula kuma a yau an halaka akalla fararen hula 5 a birnin Baquba, yayin da sojin Amirka 4 kuma suka rasu a hare-hare da dama da aka kai musu.