1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya gana da sarki Abdallah na Jordan a birnin Amman.

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bul0

Sarki Abdallah na ƙasar Jordan, ya gana yau da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan a birnin Amman, inda ya yi ikira ga Isra’ila da ta rushe kangiyar da take yi wa Lebanon. Sarkin da Kofi Annan dai sun nanata muhimmancin da akwai na aiwatad da ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta zartar kan Lebanon cikin gaggawa.

Kofi Annan na bulaguro a Gabas Ta Tsakiyan ne, don neman goyon baya ga shirin aiwatad da ƙa’idodjin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cim ma, tare da shiga tsakanin Majalisar Ɗinkin Duniyar, don kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe makwanni huɗu ana yi tsakanin Isra’ila da Hizbullahi. A yau ɗin ne dai Kofi Annan zai tashi zuwa Siriya, a ci gaban ziyararsa.

A halin da ake ciki dai, Isra’ila ta ce ba za ta rushe kangiyar da take yi wa Lebanon ba, sai an aiwatad da duk ƙa’idojin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cim ma, ƙarkashin ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartar.