1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

040809 Fatah Palästinenser

August 4, 2009

Yau a birnin Bethlehem Palasɗinawa 'yan jam'iyyar Fatah ke gudanar da babban taron ƙasa karo na farko tun bayan shekaru 20.

https://p.dw.com/p/J3ON
Shugaban Palasɗinawa Mahmoud Abbas, a tsakiya, yana tafa hannu shi da wasu manyan jami'an Fatah a taron jam'iyyar da ake yi a Bethlehem.Hoto: AP

Wannan babban taro da jam'iyyar Fatah ke gudanarwa, shi ne karo na farko da ya baiwa ‘yan jam'iyyar Fatah ‘yancin zaɓen shugabanninsu tun bayan shekarar 1989. Kimanin Palasɗinwa da ke gudun hijira 2200 ne suke halartar taron. A taron na yau dai za a zaɓi ɓangarori uku da za su jagoranci tafiyar da jam'iyyar, kuma za a ƙaddamar da sabbin manufofin jam'iyyar, waɗanda suka haɗa da amincewa da samuwar ƙasashe biyu maƙotan juna wato Isra'ila da Palsɗinu, amma kuma ta bar batun yaƙi da makami domin ƙwatar ‘yanci a matsayin wani zaɓi na wucin gadi. Fuad Kukali, wani babban jami'i ne a jam'iyyar ta fatah. Ya bayyana ra'ayinsa na mai cewa; "Muna tsammanin cewa yaƙi da makami a yanzu ba zai sa mu cimma burin da muka sa a gaba ba, amma dai duk da haka mun bar shi a matsayin wani zaɓi na wucin gadi a gare mu, kuma zamuci gaba da tattaunawa akansa."

Jami'an jam'iyyar sun ce, sabbin manufofin jam'iyyar sun yi kira ga wani sabon salo na jajircewa akan wasu ɗabi'u da Yahudawa ke yi a yankin Palasɗinawa, kamar jajircewa wajen ƙalubalantar faɗaɗa matsunan Yahudawa a yankin Palasɗinawa da kuma ganuwar da Isra'ila ta gina wadda ta shingace Palasɗinawa wadda Isra'ila ke iƙirarin cewa ta gina ta ne domin tsaro, yayin da su kuma Palasɗinawa ke kallon ganuwar a matsayin ganuwar talala a gare su. Amma duk waɗannan matsaloli a cewar Fuad, za a iya warwaresu ne idan aka samu kyakkyawan tsari a tafiyar da harkokin jam'iyyar ta Fatah, inda ya ƙara da cewa; "Muna da iyakoki a cikin muƙaman wannan jam'iyya tamu, kuma ya zama wajibi a fitar da waɗannan iyakoki ƙarara domin mutane su fahimta. Shi ya sa muka ce duk mutumin da aka baiwa wani muƙami na jam'iyya, to ba za a ba shi mukami na siyasa ba, ba zai zama minista ba, ba zai zama ambasada ba, kuma ba zai zama jagoran wata tawaga da ta shafi tsaro ba."


Mahmoud al-Aoul, tsohon gwamna ne a jihar Nablus, ya kuma bayyana abin da yake gani a matsayin hanyar da ya kamata abi domin samun amincewar al'umma; Ya ce "kafin ka ci nasarar samun amincewar al'umma kana bukatar wasu siffifofi guda biyu; Na farko dai kyakkyawan tsari domin ciyar da al'umma gaba, na biyu kuma Shugabanni na gari da za su jajirce wajen tabbatar da cewa an yi aiki da manufofin."


Shugaban Palasɗinawa Mahmud Abbas, shi ne wanda ya gaji Yessir Arafat a matsayin shugaban jam'iyyar Fatah, kuma yana fatan a cikin ƙanƙanin lokaci wannan taro zai farfaɗo da gwagwarmayar da jam'iyyar fatah ta ginu akai. Babban ƙalubalen da ke gabansa shi ne, na shawo kan Palasɗinawa da Yahudawa akan su amince da Jam'iyyar Fatah a matsayin babbar ƙungiyar da za ta haifar da tabbataccen zaman lafiya mai ɗorewa a Yankin. Wadda kuma ya kamata a sa ran cewa, ta hanyar ta ne za a tabbatar da 'yantacciyar ƙasar Palasɗinu.

Mawallafi: Abba Bashir

Edita: Yahouza Sadissou