1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron kungiyyar tarayyar turai

kamalu SaniJune 10, 2008

ziyarar shugaba Bush na Amurka a slovaniya

https://p.dw.com/p/EGof
Shugaban Amurka George W. Bush, da Primiyan Sloveniya Janez JansaHoto: AP

A ranar litinin din nan ce Shugaban ƙasar Amurka George W. Bush ya fara wata ziyara ta mako guda a wasu daga cikin ƙasashen nahiyar turai; a dai dai lokacin da yake kan hanyar sa ta halartar taron shugabannin ƙungiyar tarayyar Turai (EU)

Shi dai wannan taron wanda ake gab da fara gudanar da shi a a ƙasar slovaniya a ranar talatar nan wanda fraministan kasar Janez Jansa, wanda kuma shine shugaban kungiyar tarayyar turai a halin yanzu,zai kasance mai masaukin karɓar mahalartaa taron.

Tuni dai shugaba George w. Bush na kasar Amurka yabar fadarsa dake white house domin fara wani tattaki zuwa wasu ƙasashe na ƙungiyar Tarayyar Turai da suka hada da ƙbasashen Jamus, Italiya, Faransa, Britaniya gami da slovaniyan da mujamiar Vatican.

A cikin abubuwan da akesaran Bush zai tattauna sun hada da janyo hankulan shugabanin kungiyar dasu hada hannu domin a tallafawa ƙasar Afganistan tare kuma da kara matsa lamba akan batun shirin nukiliyar kasar Iran gami da batutuwan da suka shafi tsaro da batun sauyin yanayi a duniya baki daya.

Bugu da kari jamian diplomassiyya sun bayyana hasashen su da cewar taron shugabannin na ranar talatar nan ka iya haifar da wata matsaya guda da za´a maida hankali wajen dunkulewa guri guda musamman a bangarorin da suka hada halin yanayin tsaro na duniya,ciniki,sauyin yanayi gami da samar da makamashi.

A baya ga waɗannan ma,taron zai taɓo batun dumamar yanayi gami da shirin barin kasashen dake cikin kungiyar tarayyar turai shiga Amurka batare takardar izini ba gami da haramcin shigar da kajin Amurka zuwa nahiyar turai.ko da yake a halin yanzu mambobin tsohuwar kungiyar tarayyar turai ne kadai suke da izinin shiga Amurkan in banda kasar Girka.

kazalika shugaba Bush zai kuma tattauna akan shirin batun zaman lafiyar yankin Gabas Ta Tsakiya,hauhawar farashin kayayyakin abinci gami da batun farashin mai.

Bugu da ƙari a wata sanarwar da shugaban hukumar EU ɗin Jose Manuel Barroso ya futar a ranar litinin din nan yace, yanayin tashin hauhawar farashin abinci da na mai sune suka kasance ummul abaisin yuwuwar dunkulewar tarayyar turai da Amurka a wajen taron.

shima dai ata bakin mai bada shawara ta fuskar tsaro a kasar Amurka Stephen Hadley ayayin da yake ganawa da manema labaru cewa yayi baya zaton kalamai kawai zaa tattauna a wurin taron domin kuwa lallai za a tattauna muhimman al'amura a gurin.

Bugu da ƙari shugaba George W.Bush wanda yaki amincewa da yin amfani da karfin tuwo wajen farma ƙasar Iran a yayin da ya sa du da Frime ministan israila Ehud Olmert,a inda wasu kafafan yada labarai suka labarto da cewar shugaban Israilan yana yiwa mahukuntan birnin washington ingiza mai kantu ruwa ne akan kaiwa ƙasar Iran hari.Ko da yake dai mataimakin Frime ministan Izrailan Shaul Mofaz an jiyoshi yana cewar muddin kasar iran taci gaba da shirinta na samar da makamashin nukiliya to lallai a shiye suke su farmata.

Koma dai menene a ƙarshe taron dai ana saran shugabannin zasu cimma wata matsaya guda ta fannonin tsaro,makamashi da kuma sake waiwayar batun dumamar yanayi.