1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron Majalisar Dinkin Duniya

September 21, 2010

Ban Ki-Moon yace bai kamata matsalar tattalin arziki duniya ta shafi taimakon jin kai ba

https://p.dw.com/p/PHwh
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moonHoto: AP

Shugabanni daga kimanin kasashe 140 na duniya na cigaba da gudanar da babban taron Majalisar Dinkiin Duniya a birnin New York na Amirka wanda aka shiga rana ta biyu a yau Talata domin tattauna matsalar talauci da ake fama da shi a duniya. A jawabansu daban daban yayin bude taron shugabannin sun yi alkawarin cimma kudirorin muradun karni nan da shekara ta 2015, shirin da aka kaddamar da shi shekaru goma da suka wuce. Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-Moon ya yi roko ga wakilan kasashe cewa kada matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a duniya ta sanya su karkata akalar gudunmawar jin kai daga kasashe matalauta.

" Bai kamata a kokarin daidaita kasafin kudin mu, mu juya baya ga kasashe matalauta ba. Wajibi ne mu cigaba kada mu ja da baya a kudirin da muka dauka a hukumance na taimakon raya kasa wanda ke da nufin ceton rayukan dubban miliyoyin jama'a.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

 Edita :  Umaru Aliyu