1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babbar kotun tarayya ta haramta kungiyar Hizbul Tahrir.

January 26, 2006

A zaman da ta yi jiya a birnin Leipzig, babban kotun hukuma ta taryya, ta yi watsi da karar da kungiyar Falasdinawan nan ta Hizbul Tahrir ta kai a gabanta ta kin amincewa da haramta ta da ma'aikatar harkokin cikin gida ta yi tun shekara ta 2003.

https://p.dw.com/p/Bu27
Babbar kotun hukuma ta tarayya a birnin Leipzig.
Babbar kotun hukuma ta tarayya a birnin Leipzig.Hoto: AP

Tun cikin shekara ta 2003 ne ma’aikatar harkokin cikin gidan Jamus ta zartad da kudurin haramta kungiyar Falasdinawan nanta Hizbul Tahrir. Ma’aikatar ta dau wannan matakin ne, bayan da Hukumar ’yan sandan ciki ta sanya kungiyar, wadda ta ce mai bin tsatsaurar ra’ayin islama ne, a jerin kungiyoyin da take ganin na saba wa ka’idojin kundin tsarin mulkin kasa. Jami’an ma’aikatar ta harkokin cikin gida, sun hujjanta matakin da aka dauka kan kungiyar ne da yin matashiya da wata makala da aka buga cikin wata mujallar kungiyar mai suna „Explizit“, inda aka kwatanta Isra’ila tamkar wata cuta da ta kama zuciyar duniyar musulmi, abin da kuma ya kamata a kau da ita kai tsaye. Bugu da kari kuma, an zargi kungiyar ne da yada takardun farfaganda na nuna kyama ga Yahudawa. Game da hukuncin da kotun ta yanke na tabbatad da haramta kungiyar ta Hizbul Tahrir dai, kakakinta, Wolfgang Sailer, ya bayyana cewa:-

„Ministan harkokin cikin gida, wanda shi ne kuma ke da ikon ba da umarnin haramta duk wasu kafofi, ya yi nazarin manufofin da kungiyar ta buga a takardu, inda ya tabbatar da cewa, aikin wannan kungiyar dai ya saba wa manufar inganta fahimtar juna tsakanin al’ummai. Sa’annan kuma, kungiyar na yayata yin amfani da tarzoma da tashe-tashen hankulla ne wajen sasanta duk wasu rikice-rikicen siyasa. Ministan ya dau matakinsa ne ta yin la’akari musamman, game da shirin makarkashiyar da kungiyar ke tanadin aiwatarwa kan kasar Isra’ila.“

Saboda haramtaa kungiyar da aka yi dai, an kwace duk kadarorinta, an mika su ga hukumomin tarayya. Amma duk da haka, ba ta saduda ba. Ta yi ta daukaka kara ne har zuwa babban kotun kolin ta tarayya.

A zaman da kotun ta yi don jin kararrakin kungiyar, inda wakilanta suka bayyana cewa ba su taba ba da tallafin kudi ga wata kungiyar Falasdinawa don su yaki Isra’ila ba. A nasu bangaren, jami’an ma’aikatar harkokin cikin gida da suka wakilci ministan a gun taron, sun ce kuiran da kungiyar ta yi ta yi na a kau da kasar Isra’ila daga doron kasa ma kawai, ya janyo wani yanayi na hauhawar tsamari, inda a ko yaushe rikici zai iya barkewa.

Alkalan kotun dai na daukar kungiyar ne tamkar kungiyar siyasa, amma ba ta addini ba. Sabili da haka ba ta da kariyar da kungiyoyin addini ke da shi, ta samun damar bayyana ra’ayoyinsu wajen tafiyad da harkokin addininsu. Sun kara bayyana cewa, manufar da kungiyar ta sanya a gaba, ta yin adawa da duk wani yunkurin sasanta rikicin Isra’ila da Falasdinawa ta hannunka mai sanda, ta cancanci a haramta ta a nan Jamus. Sabili da haka ne suke ganin, matakin da ma’aikatar harkokin cikin gidan ta dauka, daidai ne kuma sun tabbatad da haka, yayin da suka yi watsi da karar da kungiyar ta kai a gaban kotun.