1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu sayar da makamai don yaki a Yemen

January 20, 2018

Gwamnatin kasar Jamus ta sanar da wani sabon mataki na dakatar da sayar da makamai ga kasashen da ke da hannun a yaki da ke faruwa a kasar Yemen. Manyan kasashe irin su Saudiyya a yankin Larabawa ne dai abin ya shafa.

https://p.dw.com/p/2rCTY
Symbolbild - Panzerbataillon
Wasu daga cikin tankokin yaki kirar JamusHoto: Getty Images/S. Gallup

Kakakin gwamnatin ta Jamus Steffen Seibert, ya ce majalisar tsaron kasa ce ta tabbatar da dakatar da ba da lasisin fitar da makaman, muddin bukatar ta saba wa tattaunawar zaman lafiya da ake yi. Wannan, wani sabon salo ne gwamnatin Jamus ke dauka na ganin an kai ga kafa sabuwar gwamnati ta la'akari da tattaunawar fahimtar juna da aka tsara. Tun a shekarar 2015 ne dai wasu kasashen Larabawa ke taron dangi kan mayakan tawayen Houthi, 'yan Shi'a a Yemen.

A bara ne kasar Saudiyya ta sanar da shirin sayen makaman Jamus, sai dai Jamus na jan kafa saboda matsin da take sha daga cikin gida kan batun kare 'yancin rayuwar jama'a.