1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu tabbas kan ganawa kai tsaye tsakanin Taliban da jami´an Koriya ta Kudu

August 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuEd

´Yan tawayen Taliban sun ce har yanzu ba´a cimma wata yarjejeniya ba kan wurin da za´a tattauna kai tsaye da jami´an diplomasiya KTK wadanda ke neman a sako ´yan kasar su 21 da ake garkuwa da su a Afghanistan fiye da makonni biyu da suka wuce. Wata tawagar jami´an KTK ta na lardin Ghazni dake kudu maso yammacin birnin Kabul, inda aka sace ma´aikatan agajin na wani coci a ranar 20 ga watan yuli. Su dai ´yan Taliban na son a tattauna ne ko dai a wuraren dake karkashin ikon su ko kuma MDD ta ba da tabbacin tsaron lafiyar su idan aka gudanar da wannan tattaunawa a wani wuri daban. ´Yan Taliban sun kshe biyu daga cikin Koriyawan kuma sun yi barazanar kashe sauran idan gwamnatin Afghanistan ta ki sako firsinonin ´yan tawaye. A kuma halin da ake ciki ana ci-gaba da kokarin ganin an sako Bajamushen nan da shi ma ake garkuwa da shi a Afghanistan.