1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu tabbas kan shigar Turkiyya cikin ƙungiyar EU.

YAHAYA AHMEDNovember 21, 2006

Da ta son shugabannin ƙasar Finnland ne, wadda ita ce ke jagorancin Ƙungiyar EU a halin yanzu, da tuni an kammala batun rikicin buɗe tashoshin jiragen ruwan Turkiyya da filayen jiragen samanta ga ƙasar Cyprus, kafin taron ƙoli na ƙasashen ƙungiyar da za a yi a tsakiyar watan Disamba mai zuwa. Amma saboda cijewar da al’amura suka yi a kan wannan batun, ƙungiyar ta EU ta bai wa mahukuntan birnin Ankara wa’adi, na su cika ƙa’idodjin buɗe tashoshin ƙasarsu ga Cyprus ɗin kafin ƙarshen wannan makon, in ko ba haka ba, ba za ta ci gaba da tattaunawa kan shigar ƙasar Turkiyyan cikin ƙungiyar ba.

https://p.dw.com/p/BtxN
Tutocin ƙungiyar EU da na Turkiyya a birni n Istanbul.
Tutocin ƙungiyar EU da na Turkiyya a birni n Istanbul.Hoto: picture-alliance/dpa

A ko yaushe, idan batun ƙasar Turkiyya ya taso a ajandar tarukan Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, sai an sami wata tangarɗa. A taron ƙolin ƙungiyar da aka gudanar a cikin watan Disamban shekara ta 2004 a lal misali, sai da aka yi ta tafiyar hawainiya, kafin a yarje kan tsai da lokacin shiga shawarwari da Turkiyyan game da neman shigarta ƙungiyar da take yi. A wannan lokacin dai an tsai da ranar fara tattauanawar ne a ran 3 ga watan Oktoban shekara ta 2005. Da ranar ta iso kuma, sai da aka sami jinkiri. A galibi kuma, akasarin matsalolin da ke kunno kai, sun shafi rikicin Turkiyan ne da ƙasar Cyprus.

Game da hakan ne dai, ƙasar Finnland, wadda ke jagorancin harkokin ƙungiyar EUn a halin yanzu, take ƙoƙarin ganin ba a sami cikas ba kuma a kan shawarwarin da Turkiyyan. A wani taron maneman labarai jiya a birnin Helsinki, Firamiyan ƙasar Finnland ɗin, Matti Vanhanen, ya ce ba ya sha’awar ganin an sanya batun Turkiyyan kan ajandar taron ƙolin da shugabannin ƙungiyar EUn za su yi a birnin, a tsakiyar watan Disamba. Masharhanta dai na ganin hakan ne tamkar ƙara angaza wa Turkiyyan ke nan da EUn ke yi, don ta amince da sharuɗɗanta. Waɗannan sharuɗɗan kuwa, su ne kamar mizanin da ƙungiyar za ta yi amfani da shi, wajen auna ci gaba ko kuma cikas ɗin da shawarwarin za su haifar.

To ko mece ce bukatar EUn ga Turkiyya? Tun da farko dai, babban sharaɗin da ƙungiyar ke son ganin Turkiyyan ta bi ko kuma ta cika, shi ne faɗaɗa shacin kasuwanci maras shinge zuwa duk ƙasashe mambobinta, wato har da ma ke nan yankin girkawa na tsibirin Cyprus. Jami’an ƙungiyar a birnin Brussels sun bai wa Turkiyyan wa’adi ne har zuwa ƙarshen wannan shekarar, da ta amince wa Cyprus ɗin yin amfani da sararin samaniya, da filayen jiragen samanta da kuma tashoshin jiragen ruwanta. A ganin mahukuntan birnin Ankara kuwa, cika wannan ƙa’idar ya zo daidai ke nan da amincewar ƙasar Turkiyyan da wanzuwar Cyprus ɗin tamkar ƙasa, abin da har ila yau take watsi da shi. A nata ɓangaren, Turkiyyan na bukatar EUn ne da ta ɗau matakan ganin cewa, an sassauta saniyar waren ƙasa da ƙasa da ake yi wa ɓangaren Turkawa na arewacin tsibirin na Cyprus. Ankara na neman wannan yankin ne ya fara hulɗoɗi kai tsaye da ƙungiyar EUn ba tare da wani shinge ba. To sai dai har ila yau, a fagen siyasar ƙasa da ƙasa, ba a amince da yankin tamkar ƙasa mai zaman kanta ba. Ita kuma nahiyar Turai, wato EUn, tana nanata cewa, batutuwa daban-daban ne da suka bambanta da juna, kuma bai kamata a haɗa su a waje ɗaya ba.

To yanzu dai, ita ƙungiyar EUn ta bai wa Turkiyya wa’adi na ta cika waɗannan ƙa’idojin kafin ƙarshen wannan watan Nuwamba da muke ciki. Saboda a taron da za su yi a ran 11 ga watan Disamba mai zuwa ne, ministocin harkokin wajen ƙungiyar za su yanke shawara kan makomar ci gaban tattaunawar da Turkiyya.

Babban jami’in ƙungiyar EUn mai kula da batun faɗaɗa ta, Olli Rehn, ya ce Hukumar ƙungiyar za ta bai wa taron ƙolin shugabanninta shawara ne kan yadda za a tinkari wannan lamarin, idan Turkiyyan ba ta cika ƙa’idojin ba:-

„Za a yi taron ƙarshe na hukumar ne kafin ran 11 ga watan Disamban, wato a ran 6 ga wannan watan. Wannan lokacin ne kuma ya dace da hukumar ta miƙa shawararta, idan Turkiyyan ba ta cika ƙa’idojin ba kafin cikar wa’adin da aka ba ta.“

Ita ko gwamnatin Turtkiyyan, har ila yau ta dage ne kan cewar ba za ta kauce daga manufarta game da tsibirin Cyprus ɗin ba. Muddin ba a kawo ƙarshen saniyar waren da ake yi wa yankin arewacin tsibirin mai rinjayin Turkawa ba, to mahukuntan birnin Ankara ba za su ɗau kon wane mataki ba kuma.