1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baje kolin zanen yaran Darfur a Berlin

Hauwa Abubakar AjejeMarch 15, 2007

Gidan nuna kayaiyakin tarihi na yahudawa dake Berlin tare da hadin gwiwar kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ta Human Rights Watch sun kaddamar da kanfe na mako guda kan batutuwan take hakkin bil adama a lardin darfur na kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/Btvz
Hoto: Jüdisches Museum Wien/PID/Votava

: Dakin nuna kayan tarihin na yahudawa tare da HRW suna son janyo hankalin jamaar duniya ne game da daya daga cikin rikici mafi muni a duniya,kamar yadda jamiar HRW dake gudanar da bincike kan halinda ake ciki a Darfur Leslie Lefkow ta baiyanawa DW.

„tace manufar wannan babban taro itace kara janyo hankalin jamaa game da take hakkin bil adama dake faruwa a darfur.Kamar yadda kuka sani ana ci gaba da tursasawa jamaa tare da aikata laifukan yaki cikin yan shekarun nan,saboda haka taron yana son duba halinda ake ciki tare da nufin tattauna matakai da suka dace a dauka wajen kawo karshen rikicin.“

A wannan biki zaa nuna zane zane da yara kanana na darfur sukayi game da halinda suke ciki dama yankin baki daya,Leslie tace hakan zai nuna yadda rikicin ya shafi tunanin yara kanana da abin ya rutsa da su.

„tunanin yin hakan ya zone saaboda gidan tarihin yana bukatar baje zanen da yaran sukayi,wadanda kuma HRW ta tattara su daga yara a Darfur da Chadi,wadannan zane zane da yara kanana yan shekaru dabam dabam sukayi,sun baiyana a fili irin azaba da gwamnatin Sudan takeyiwa farar hula a Darfur“

A bikin na mako guda kungiyoyi da dama kamar gamaiyar kungiyoyi kan kudancin Sudan da HRW da hukumar abinci ta MDD da kuma kungiyar likitoci ta DWB zasu mika kasidu game da halinda ake ciki a Darfur,bisa bayanai da bubuwan da suka ganewa idanunsu.

Tsohon sakataren MDD Kofi Annan wanda shine bako na musamman a wajen wannan biki a sakonsa ya koka da yadda kasashen duniya sukayi kunnen uwar shegu game da halinda ake ciki a Darfur.

Yace har yanzu babu wani darasi da aka koya daga abubuwab da suka faru a Bosnia da Rwanda.

Za a kwashe mako guda ana baje hotuna da zane zane na halin ukuba da ake ciki tare da mika kasidu da jawabai daga wadanda suka ganewa idanunsu halinda ake ciki a Darfur.