1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baki sun fuskanci turjiyar jami'ai a Pretoria

February 24, 2017

'Yan sandan Afirka ta Kudu sun afkawa gungun baki lokacin wani gangami a birnin Pretoria.

https://p.dw.com/p/2YCzb
Südafrika Pretoria Unruhen wegen Migranten
Hoto: AFP/Getty Images

Rahotanni daga Pretoria babban birnin kasar Afirka ta Kudu sun ce 'yan sandan kasar sun yi amfani da albarusan roba da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar cin zarafin baki da yan kasar ke yi, a wani babban gangami da aka yi wannan Juma'a a birnin. An dai ga 'yan sandan kwantar da tarzoma cikin jerin gwano inda suka nufi wani gungu na akalla mutum dubu guda da suka fito suna macin nuna fushin kyamar ta su, akasari kuwa 'yan nahiyar Afirka da ke a kasar.

Shaidu sun ce cikin makonni 2 da suka gabata 'yan kasar Afirka ta Kudu sun kwashe dumbin dukiyoyin 'yan kasashen wajen. Hankulan baki 'yan kasashe irinsu Najeriya da Zimbabwe da Somalia dama Pakistan sun yi matukar tashi kan hare-haren da 'yan Afirka ta Kudun ke kai masu.

'Yan sandan dai sun raunata da dama daga cikin masu nuna fushi kan kyamar da ake masun. Ana dai zargin bakin da dillancin kwayoyi a kasar. Kuma 'yan kasar masu yawa na goyon bayan aikin 'yan sandan na wannan Juma'ar.