1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Balaguron Benazir wajen karachi na farko

October 27, 2007
https://p.dw.com/p/C15Z

Shugabar adawa ta Pakistan, Benazir Bhutto tayi balaguro izuwa Mahaifarta dake kudancin kasar, don ziyara da kuma yakin neman zabe.Balaguron yazo ne kwanaki kadan bayan bayan harin da aka kai mata a Karachi, wanda bai samu nasara ba.Daruruwan magoya bayan ta ne suka je taryarta, a filin jirgin saman Sukkur dake kudancin kasar. Bayanai sun nunar da cewa daruruwan jami´an tsaro aka jibge, a filin jirgin saman, don tabbatar da tsaro da oda a lokacin ziyarar tata. Rahotanni sun tabbatar da cewa Benazir Bhutto a shirye take ta ci gaba da yakin neman zaben, don samawa jam´iyyar ta PPP matsayi a zaben na gama gari.Wannan dai shine karo na farko da tsohuwar faraministar tayi balaguro izuwa wajen birnin Karachi, a tun bayan isar ta kasar, shekaru takwas tana gudun hijira.