1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bama-bamai sun fashe a birnin Ankara

May 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuKq

Wasu bamai bamai sun fashe yammacin yau, a birnin Ankara na ƙasar Turkiyya, wanda kumasu ka hadasa mutuwar mutane 5 da jikita wasu fiye da mutane 60.

Praminsitan ƙasar Turkiyya Recep Tayib Erdowan, ya ɗora alhakin wannan hari, ga ƙungiyoyin ta´adanci.

Bama-baman sun tarwatse a cikin wata kasuwa, da ke unguwar Ulus, dake tsakiyar birnin Ankara.

A halin da ake ciki, jamai´an tsaro, sun yi wa wannan unguwa zobe, da zumar capke wanda ke da alhakin kai wannan hari.

A shekarun baya-bayan nan, ƙasar Turkiyya, ta fuskanci hare-hare, daga ƙungiyoyi daban-daban, da su ka haɗa da ƙurdawa yan aware, da masu tsatsauran ra´ayin addinin islama.