1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bama bamai sun tashi a Iraqi

August 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuDm

Wani bom ya tashi a arewacin yankin Kirkuk dake Iraqi, inda nan take mutane hudu suka rasu wasu kuma 37 suka jikkata. Irin wannan idan an iya tunawa shine ya faru ga arewacin kasar, wanda hakan yayi ajalin mutane kusan dari biyu.Hakan ya haifar Mdd yin Allah wadai da wadanda keda hannu a cikin tashin tagwayen bama baman.Bugu da kari Mdd ta kuma bukaci yan kasar dasu hada dai, domin kawo karshen wadannan tashe tashen hankula da kuma rikice rikice. A yanzu haka dai gwamnatin Faraministan Nuri Al Maliki na kokarin daidaita sahu ne, na kafa gwamnatin hadaka. Samun hakan a cewar masu nazarin abinda kaje yazo, itace hanya daya da zata taimakawa wajen tabbatar da doka da kuma oda a kasar.Rahotanni dai sun shaidar da cewa tattaunawar cimma sulhu a tsakanin gwamnatin ta Nuri Al Maliki da yan Sunni na nan naci gaba da gudana a yankin Tikrit, mahaifar marigayi Saddam Hussain.