1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-Moon ya isa birnin Juba a Sudan ta Kudu

Salissou BoukariFebruary 25, 2016

A cikin ziyarar da ya ke a wasu Kasashen Afirka, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ban Ki-Moon ya isa Sudan ta Kudu a wannan Alhamis.

https://p.dw.com/p/1I1j6
Ban Ki-moonHoto: Reuters/T. Negeri

Yayin isowar sa a kasar ta Sudan ta Kudu sakataran na Majalisar Dinkin Duniya ya samu tarbo a filin jirgin sama na Juba babban birnin kasar daga Ministan harkokin wajan kasar Barnaba Marial Benjamin kafin daga bisani ya gana da shugaban kasar Salva Kiir inda za su tattauna batun yakin basasan da ya daidaita kasar tun daga watan Disamba na 2013, da kuma batun aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a watan Augusta na 2015 tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a kasar.

Ana sa ran batun harin da aka kai na ranekun 17 da 18 ga wannan wata na Febrairu a sansanin 'yan gudun hijira na Malakal da ke karkashinMajalisar Dinkin Duniya zai shigo cikin tattaunawar.