1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-Moon yayi Allah wadai ga sabbin gine gine a yankunan Palestinu da Isra´ila ta mamaye

March 10, 2010

Ban Ki- Moon ya bayana damuwa ga sabin mamayen Isra´ila a yankunan Palestinu.

https://p.dw.com/p/MOWC
Ban Ki-MoonHoto: AP
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin ɗuniya Ban ki-Moon yayi Allah wadai ga matakin da ƙasar Isra´ila ta ɗauka na yin wasu sabbin gine gine 1600 a yankunan da ta mamaye a yankin yama ga kogin Jordan .Tun can da farko dai kafin kalamun na Ban ki-Moon, mataimakin shugaban Amirka ne Joe Biden da ke yin ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya ya nuna damuwarsa akan sabbin gine gine na Isra´ila a yankin ƙudus ta gabas.Wani kakakin Majalisar Ɗinkin Duniyar  Martins Nesirky ya shaida cewa wannan yunƙuri na Isra´ila na taka dokokin da aka cimmawa na ƙasa da ƙasa zai sake mayar da shirin zaman lafiyar  baya da ake ƙoƙarin cimma a yankin na Gabas ta Tsakiya   abinda kuma ya ce ba alheri ba ne ga ƙasar ta Isra´ila . An shirya dai nan gaba ƙadan Mista Ki-Moon zai ziyarci ƙasar ta Isra´ila da yankin Gokin Jodan da kuma yankin Gaza.Tun can da farko dai ƙasashen Isra´ila da Palesɗinu sun amince da wani shirin tattaunawa na watannin huɗu a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya,a ranar litinin ne da ta gabata ministan harakokin tsaro na Isra´ila ya bayar da izini ga Ban Ki-Moon da wakiliyar ƙungiyar Tarayya Turai kan harakokin waje Catherine Ashton da su kai ziyara a yankin na Gaza.

Mawallafi: Abdurrahman Hassane Edita: Yahouza Madobi