1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon yayi kira ga larabawa su goyi bayan shirin zaman lafiya na Amurka a Gabas ta tsakiya...

March 27, 2010

Sai dai shugaban Palasɗinawa Mahmud Abbas yace ganawar ƙeƙe da ƙeƙe da Isr'ila ba zata saɓu ba

https://p.dw.com/p/Mft5
Ban Ki-moon tare da Amr Moussa a taron LarabawaHoto: AP

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon yayi kira ga shugabannin Larabawa su goyin bayan shirin Amurka na zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasɗinawa. A lokacin da yake jawabi wajen wani taron shugabannin larabawa da aka fara yau a birnin Sirte, na ƙasar Libya,  Ban Ki-moon yace ko yaya takai ta kawo hanya ɗaya ta wanzuwan ƙasar Palasɗinu itace ta samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya tare kuma da samun haɗin kan ƙasashen larabawa. Tuni dai shugaban Palasɗinawa Mahmud Abbas yace ganawar ƙeƙe da ƙeƙe da Isra'ila ba zata saɓu ba, har sai Isra'ilan ta dakatar da shirin ta na gine-gine a yankin gabashin birnin ƙudus. A jawabin sa babban sakataren ƙungiyar ƙasashen na Larabawa Amr Moussa kira yayi ga ƙasashen na larabawa dasu shirya fitar da wani sabon hanyar samun zaman lafiyan yankin, bisa la'akari da rugujewar shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasɗinawa a kowane lokaci daga yanzu. Yanzu haka dai rahotannin dake fitowa daga kanfanin dillancin labaran Reuters na cewar dakarun dakarun sojin Isra'ila sun janye daga yankin kan iyakar ƙasar da Gaza bayan wani bata kashi da akayi tsakanin ɓangarorin biyu ya haifar da mutuwar Sojojin Israila biyu da kuma na Hamas biyu. A jiya ne dai Firaminista Israila Benjamin Netanyahu ya gana da majalisar ministocin sa da nufin tattauna kace nacen dake wakana tsakanin Isra'ila da Amurka, sakamakon matakin Isra'ilan na cigaba da gina sabbin matsugunai a yankin gabashin birnin ƙudus.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed Abubakar