1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon yayi kiran samun adalci a zaɓen Guinea.

June 26, 2010

Wannan ne karon farko na gudanar da zaɓe a Guinea tun bayan samun 'yancin kai

https://p.dw.com/p/O45X
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki-moonHoto: AP

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon yayi kiran samun adalci a zaɓen ƙasa da za'a gudanar gobe lahadi a Guinea.

A sanarwar da Babban Sakataren na Majalisarɗinkin duniya Ban Ki-moon ya fitar yayi fatan zaɓen wanda shine na farko cikin shekaru fiye da Hamsin, zai kasance abin misali ga sauran ƙasashen Afirka.

Don haka yayi kira ga ɗokacin jam'iyu da hukumomin gwamnati da sauran ƙungiyoyin taimakon ƙasa da zasu saka ido a zaɓen su haɗa kai da juna domin samun nasarar sa. Sanarwar Babban Sakataren ta zo ne a dai dai lokacin da aka samu rahoton ɓarkewar rikici a ranar alhamis wanda ta hallaka mutum guda.

Kanfanin dillancin labaran faransa ta ruwaito cewar kimanin masu kaɗa ƙuri'a miliyan huɗu ne ake fatan zasu kaɗa ƙuri'un nasu ga 'yan takara 24 a zaɓen shugaban ƙasa na farko tun samun 'yancin ƙasar a shekarar 1958.

Mawallafi:Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed Abubakar