1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangarori a Somalia sun amince da shawarar da Yemen ta mika

June 16, 2006
https://p.dw.com/p/Butr

Shugabbanin kungiyar Islama dana gwmantin riko a kasar Somalia sun baiyana goyon bayansu ga shawarar da kasar Yemen ta bayar na tattaunawa domin kawo zaman lafiya a kasar.

Wani jamiin kasar ta Yemen yace,shugaban kungiyar ta Islama Sheikh Shariff Ahmed tare da shugaban riko Abdullahi Yusuf Ahmed,sun amince da batun tattaunawa a cikin kasar ta Somalia ko wata kasa makwabciya a lokacin wata tattaunawa da shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh ta wayar tarho.

Kasar Yemen ta mika tayin shiga tsakani ne yayinda magoya bayan kotunan musulunci suka kame wasu yankuna na kasar.

A halin da ake ciki kuma taron kasashe masu tuntubar juna akan rikicin kasar Somalia yayi kira ga bangarorin dake yaki da juna da su baiwa maaikatn agaji damar kaiwa ga jamaar kasar da suka tagaiyara.

Amurka tare da kasar Norway suka karbi bakuncin taron.

Zaa gudanar da taro na gaba a kasar Sweden inda kungiyar kasashen ta shirya gaiyatar Majalisar Dinkin Duniya da AU da kungiyar kasashen larabawa da kuma kungiyar IGAD wadda ta taimaka kafa gwamnatin rikon kwarya ta Somalia a matsayin masu sa ido a taron.