1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankado kitsa harin ta'addanci a Najeriya

December 8, 2017

Rundunar 'yan sandan kasar ta fitar da sanarwar gargadin al'umma cewa bayanai na sirri da ta samu na tabbatar da mayakan Boko Haram na shirin kaddamar da munanan hare-hare musamman na kunar bakin a wasu jihohin kasar.

https://p.dw.com/p/2p1SH
Nigeria Frank Mba
Hoto: picture-alliance/dpa

Dama dai Kungiyar Boko Haram kan kai hare-hare irin na kunar bakin wake a wuraren da jama'a ke taruwa don yin ibada ko bukukuwa a irin wannan lokaci, duk matakai na tsaro da ake da su musamman a jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ma birnin tarayya Abuja. Domin ankarar da mutane da kuma nunar da su muhimmancin kula da sa-ido wajen taya jami'an tsaron aiki, ya sa rundunar 'yan sandan Najeriya fitar da sanarwa ta gargadin yiwuwar kai hare-hare a irin wannan lokaci. 

Rundunar 'yan sandan ta bukaci jama'a su kasance masu sa-ido tare da kai rahoton duk wani da su gane take-taken sa ba, inda a nata bangaren ta ce za ta yi bakin kokari wajen ganin ta dakile duk wani hari da mayakan ka iya kaiwa.
Kokarin da na yi don jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan don jin karin bayani kan wannan gargadi ya ci tura, don na buga wayarsa bata shiga kuma ban samu amsar sakon kar ta kwana da na aike masa ba.

Symbolbild Nigeria Polizei
Hoto: imago/Xinhua

Ko me ya kamata al'umma su yi a wannan lokaci domin yi wa kan su kiyamu-laili daga hare-hare? Tambayar da wakilinmu Al-Amin Suleiman Muhammad ya yi wa Malam Muhammad Matawalle, mai fashin baki kan harkokin tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya. Wanda ya ce ya zama wajibi ne jama'a kada su saki jiki bisa ganin an samu dawowar zaman lafiya.

Wannan gargadi dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da bukuwan Mauludi da kuma shirin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, abin ke haifar da fargaba a zukatan al'umma. Malam Ibrahim yarima wani dan gudun hijira da ke nan a birnin Maiduguri, ya ce suna fama da fargaba kam, kuma addu'a ce kawai za ta fitar da al'umma daga wannan barazana.

Na tambayi Bishop Naga Muhammad, shugaban Kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Borno, ko akwai mataki da suke dauka na kare al'umma daga irin wadan nan hare-hare da ake hasashen samu a irin wannan lokaci. Ya ce dama a nasu bangaren basu saki jki ba, sai dai gwamnati ce ke da karfin kare jama'a.

Sai dai gwamnan jihar Borno Kashim Shetima, ya ce babu wata barazana da 'yan kungiyar za su yi, da zai sa al'umma su sauya rayuwar su ta yau da kullum. Tuni dai jama'a suka fara taka tsantsan a wuraren hada-hadarsu. Kuma tuni wasu wurare suka fara binciken kwakwab ga masu shiga ko fita kasuwanni da wasu wuraren ibada, don tabbatar tsaro kamar yadda rundunar 'yan sandan ta shawarce su.