1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankunan raya kasa zasu bawa Gambia rance

December 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvFb

Wasu bankunan raya kasa guda uku , sun shaidar da cewa a shekara mai zuwa zasu bawa kasar Gambia rancen kudi da yawan su ya tasamma dalar amurka miliyan 19, don samar da hasken wutar lantarki ga kauyuka kusan hamsin a kasar.

Wadan nan bankuna dai a cewar Ministan kudi da tattalin arziki na kasar,wato Musa Bala Gaye sun hadar da bankin raya kasashen Afrika, ADB da bankin Islama na raya kasashe, IDB da kuma bankin raya kasashe daci gaban tattalin arzikin su na Afrika, wato ABCDF.

Ministan ya kara da cewa an cimma wannan matakin ne a tsakanin wadan nnan bankuna uku da kuma bangaren gwamnatin kasar ta Gambia ne a jiya litinin.

Rahotanni dai sun nunar da cewa gwamnati a kasar ta Gambi ta damu kwarai da aniya wajen inganta harkar wutar lantarki a kasar dake fuskantar matsaloli nan da can.