1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barack Obama zai nemi tsayawa takara a karkashin jam´iyar Democrat

February 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuS4

Dan majalisar dattijan Amirka Barack Obama ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugabancin Amirka a karakashin inuwar jam´iyar Democrat a shekara ta 2008. Obama ya bayyana haka ne a wani jawabi da yayi a gaban magoya bayan sa a babban birnin jihar Illinois, Springfield wurin da Abraham Lincoln ya yi kira da a kawo karshen bautar da bakar fata. Obama ya kuduri aniyar zama shugaban Amirka na farko bakar fata.

„Na tsaya ne a gaban ku yau domin in sanar da ku niya ta ta tsayawa takarar neman shugabancin kasar Amirka.“

Obama dai yayi alkawarin jagorantar abin da ya kira sabon jini na shugabanci wanda zai kara karfafa matsayin Amirka. A game da Iraki kuwa ya ce yanzu lokaci yayi da ya kamata dakarun Amirka su koma gida. Ana ganin Obama a matsayin daya daga cikin ´yan gaba-gaba da zasu nemi jam´iyar Democrat ta tsayar da su ´yan takararta da zasu nemi shiga fadar White House. Daga cikin su kuwa akwai Hillary Clinton uwargidan tsohon shugaban Amirka Bill Clinton.