1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baraka a kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC

Uwais Abubakar Idris daga AbujaMay 17, 2016

Wani bangare na kungiyar kwadagon Najeriya wato NLC ya bayyana cewa ba zai shiga yajin aikin da uwar kungiyar ta kira dangane da karin kudin mai ba.

https://p.dw.com/p/1IpDe
Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010
Hoto: dapd

Wannan baraka a tsakanin kungiyar kwadagon Najeriyar da ke kara fitowa fili, bayan da bangaren Joe Ajaeron na kungiyar kwadagon Najeriyar ya nuna adawarsa da yajin aikin da uwar kungiyar ta kira sakamakon janye tallafin man fetur da hukumomi suka yi. Wannan bangare na kungiyar dai ya kunshi ma'aikatan wutar lantarki da na man fetur da ke da tasiri sosai a duk wani yajin aiki da ya shafi karin kudin mai a kasar.

Da ya ke tsokaci kan mataki da suka dauka, Kwamared Nasiru Kabir da ke magana da yawun kungiyar kwadagon bangaren Joe Ajaeron wadanda adawa da yajin aikin, ya ce wannan cire tallafin mai da aka yi abu ne da nan gaba zai zame wa kasar alheri, kuma a wannan lokacin wanda ke cikin gwamnatin kasar mutane ne masu amana sabanin wanda ake da su a baya lokacin da aka yi yunkurin cire tallafi na gwamnatin Goodluck Jonathan.

Nigeria Tankstelle in Lagos
Kungiyar kwadagon Najeriya ta ce karin kudin mai zai jefa talaka cikin kunci.Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

To sai dai ga shugaban kungiyar kwadagon Najeriyar Kwamared Ayuba Waba ya ce janye tallafin man da gwamnati ta yi wanda ya haifar da tashin kudin man fetur a kasar zuwa Naira 145, zai yi tasiri marar kyau ga rayuwar talakawan Najeriya wanda dama suke cikin yanayi na kunci sakamakon matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.

1. Mai-Kundgebung in Abuja
Baraka a kungiyar kwadagon Najeriya na barazana ga yajin aikin da aka shirya yi ranar LarabaHoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Wannan ne dai karon farko da baraka a tsakanin kungiyar kwadagon Najeriyar ke zama babbar matsala a gareta domin kuwa a lokutan baya kungiyar kan kasance tsintsiya madaurinki daya a game da batu na yajin aiki. Yanzu haka dai 'yan Najeriya sun zuba idanu don ganin yadda lamarin yajin aikin zai kasance dai-dai wannan lokacin da baraka a cikin kungiyar ke cigaba da wakana.