1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barayin shanu sun halaka mutane a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
February 16, 2018

Wasu kafafan yada labarai na cewa mutanen da suka rasu a farmakin da aka kai a jihar Zamfara sun kai 40. Lamarin da ke kara lalacewar tsaro a kasar.

https://p.dw.com/p/2soQ4
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

'Yan sanda sun bayyana cewa mutane 18 ne suka rasu a jihar Zamfara Arewa maso Yammacin Najeriya. Mai magana da yawun 'yan sanda a jihar Muhammad Shehu ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi kwantan bauna da halaka al'umma a kauyen Birani a lokacin da suka je kauyen a kokari na satar shanu, yunkurin da ya fiskanci turjiya ta al'umma.

Wasu kafafan yada labarai na cewa mutanen da suka rasu fa sun kai 40. Wannan dai shi ne na baya-bayan nan cikin jerin kashe-kashe da ake yi a kokarin 'yan bundiga na satar shanu a kauyikan da ke a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa dubban al'umma ne aka rabasu da muhallansu yayin da a ka kashe a kalla mutane 168 tun da wannan shekara ta kama a rikicin da a ke samu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihohi biyar na Najeriya.