Barazanar ɓarkewar saban rikici a Sudan
October 10, 2010A yayin da ya rage watani uku kacal a shirya zaɓen raba gardama na neman yancin kan yankin kudancin Sudan, alamu na ƙara nuna sake abkuwar wani saban faɗa tsakanin gwamnatin Sudan da tsafin´yan tawayen SPLM.
A wani jawabi a ya gabatar jiya birnin Syrthe na ƙasar Libiya shugaban ƙasar Sudan Omar Hasan Al Bashir ya zargi SPLM da yin fatali da wasu daga ƙa´idodin yarjejeniyar zaman lafiya da su ka rattaba wa hanu a shekara 2005.
Jawabin na shugaba Albashir ya bayyana buƙatar sake saban zama, domin tattana wannan matsaloli, matakinda yankin kudancin Sudan ya yi watsi da shi.
A wannan mako Komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tura tawaga ta mussamman a yankin Kudancin Sudan domin gani da ido inda aka kwana game da shirye-shiryen wannan zaɓe.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmed Tijani Lawal