1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar lakabawa yan tawayen Kongo takunkumi

Hauwa Abubakar AjejeDecember 22, 2005

Komitin sulhu na majalisar dinkin duniya,ya sake sabunta bukatarsa cewa,dukkan kungiyoyi na ketare dake goyon bayan kungiyoyin tawaye na Jamhuriyar Demokradiyar Kongo,da su ajiye makamansu,ya kuma yi barazanar lakabawa shugabanninsu takunkumi.

https://p.dw.com/p/Bu38
Hoto: AP

Cikin wani kudiri da ta dauka,komitin sulhun mai membobi 15,yayi kira ga dukkan kungiyoyi masu dauke da makamai na yankin,wadanda suka hada da,kungiyar FDLR ta yan kabilar Hutu a Rwanda,da kungiyar yan tawayen hutu dake Burundi da kuma yan bindiga na LRA ta Uganda,da cewa,su ajiye makamansu ba tare da bata lokaci ba,su kuma shiga cikin shirye shiryen tarwatsa kungiyoyin nasu tare da bada goyon bayansu ga kokarin samarda zaman lafiya a wannan yankin na Afrika.

Komitin ya yanke shawarar cewa,daga watan yuli na shekara mai zuwa,zai fara dora takunkumi da zasu hada da,haramta tafiye tafiye da dakatar da kadarori,na shugabannin siyasa dana sojin kungiyoyi masu dauke da makamai wadanda suka kasa kwance damarar yakin dakarunsu ko kuma hana su yin hakan.

Hakazalika,takunkumin zai shafi shugabannin kungiyoyin yan tawaye na Kongo da suke samun taimako daga wasu kasashe,musamman kungiyoyin da suke lardin Ituri.

Komitin sulhun,ya kuma bukaci gwamnatocin kasashen,Uganda,Rwanda,Jamhuriyar Demokradiyar Kongo da Burundi,da su dauki matakan kawo karshen yin anfani da bakin iyakokinsu ana karya dokar hana shigo da makamai da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa.

Ya kuma bukaci kasashen dake makwabtaka da Janhuriyar Demokradiyar Congo ciki har da Kongo Kinshasa,da su dakatar da duk wani goyon baya ga yin anfani da albarkatun kasa na Kongo ba bisa kaida ba,musamman hana wucewa da irin wadannan albarkatu ta cikin kasashen makwabta.

Komitin sulhun,ya kuma yaba da yadda aka gudanar da kuriar raba gardama akan kundin tsarin mulkin kasar,wanda ya amince gudanar da zabe a watan yuni na shekara mai zuwa.

A wani labarin kuma,wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya,ya sanar cewa,dakarun majalisar dana Kongo sun kai dauki kan wata kungiyar tawaye a kasar,a kokarinsu na dawo da ikon gwamnati a lardin.

Inda yace dakarun majalisar 375 da kuma na Kongo 1,500,suka kai daukin a akan yan tawayen kabilar Lendu karkashin shugabansu Peter Karim a arewacin Bunia dake lardin Ituri.

Dakarun na Majalisar Dinkin Duniya suna kokarin wanzar da zaman lafiya ne a jamhuriyar demokrdiyar Kongo bayan yakin basasa na shekaru biyar da yayi sanadiyar rayukan mutane akalla miliyan 4,musamman sakamakon yunwa da cututtuka.

Yakin dai ya kawo karshe a 2003,amma an samu yan kungiyoyi dabam dabam da suke matsawa farar hula musamman a gabashin kasar inda ake da albarkatun kasa da dama.

Bayan suka da ta sha na kasa kare farar hula a lardin Ituri ,Majalisar Dinkin Duniya a wannan shekarar,ta kara yawan dakarunta ta kuma inganta aiyukanta a lardin,inda ta dauki sabbin sojoji 15,000, membobin tsoffin kungiyoyin tawaye na kasar,kodayake ana ganin cewa akwai dubban su har yanzu a cikin dazuzukan kasar.

A ranar lahadi da ya gabata ne,Kongo ta samu nasarar gudanar da kuriar raba gardama akan kundin tsarin mulkin kasar,wadda ya bada damar zabe cikin watanni 6 masu zuwa karkashin wata yarjejeniya da aka cimamawa a 2003.