1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar Murar tsuntsaye wa biladama a Nigeria

February 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuS2

Duk dacewa baaa sake samun batun cutar murar tsuntsaye a jikin biladama,bayan wadda ta ritsa da ran wata mata a jihar Lagos ba,anyi gargadi dangane da daukan matakai na kariya musamman a yankunan baa san barazanar kamuwa da irin wannan cuta ba.Mr Tony Forman dan kasar Australia dake aiki da hukumar kula da harkokin noma da abinci ta mdd,ya fadawa manema labaru a birnin Lagos cewa kauracewa cutar daga tsuntsu zuwa biladama yafi hadari ne a kasashenda alummominsu ke nuna halin ko oho da hakan.Ya bayyana cewa halin da Nigeria take ciki da irin yawan alummominta,yazo daidai da wasu kasashe a nahiyar Asia.A wannan watan nedai hukumar kula da lafiya ta mdd ta tabbatar da cutar murar tsuntsaye a jikin wata mata data rasa ranta,wanda ke zama irinsa na farko a Nigeria dama yammacin Afrika baki daya.