1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar' tashin dutse mai aman wuta a Indunusiya

August 29, 2010

Gwamnati a ƙasar Indunusiya ta ɗauki matakai na kariya a sakamakon bore da wani dutse mai aman wuta ya fara

https://p.dw.com/p/Oyyq
Hoto: AP

Hukumomi a ƙasar Indunesiya sun ƙwashe aƙalla mutane dubu goma sha biyu daga wani yanki da ke kan tsauni a arewacin ƙasar a tsibirin Sumatra a sakamakon bore da wani dutse mai aman wuta ya fara yi, wanda kuma shi ne karo na farko da ya fara tayar da hayaƙi da kuma fitar da toka tun shekaru 400 da suka wuce.

Dutsen wanda ake kira da suna Sinabung, wanda kuma hayaƙinsa ya turniƙe sararin samaniya har ya zuwa mile dubu da ɗari biyar ya sa jama'ar ƙasar cikin shirin ko ta ƙwana.

Ministan kiwon lafiya na ƙasar wanda ya shaida cewa babu wani mumunan haɗari da ke da akwai ya zuwa yanzu akan barazanar' dutsen ya ce sun ɗauki matakan kariya na kiyaye al'uma.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane

Edita : Ahmad Tijani Lawal